News
Karin Albashin Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi Da Kaso 25 Zuwa 35 Cikin 100 Ga Ma’aikatan Kasar Nan, Ya Yi Matukar Kadan
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Injiniya Sani Bala ya ce a ra’yinsa karin Albashin ba zai wadaci Ma’aikata wajen gudanar da bukatunsu na yau da kullum.
Nan kuma engr Sani Bala ya ce karin Albashin da gwamnatin tarayya ta yi da kaso 25 zuwa 35 cikin 100 ga Ma’aikatan Kasar nan, ya yi matukar kadan.
Tarihin Abubuwan Da Suka Auku A Rana Irin Ta Yau 11 Ga Watan Mayu
Injiniya ya kara da cewa la’akari da bukatun yau da kullum da kuma tashin farashin kayayyaki, Karin da aka yiwa Ma’aikatan babu abunda zai yi masu.
A saboda haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake yin nazari kan karin Albashin domin yin abunda ya dace, a hirarsa da Arewa radio.
injiniya Sani Bala wanda shine shugaban kwamitin ma’aikata a Majalisar wakilai, ya ce la’akari da yanayin da kasa take ciki, Ma’aikacin gwamnati na bukatar samun gyara a Albashinsa.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
