News
Wata sabuwar cuta da ba’asan ta ba ta halaka mutane 4, tare da wasu mutane 177, da suka kamu a jihar Zamfara.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wata sabuwar cuta da ba’asan ta ba ta halaka mutane 4, tare da wasu mutane 177, da suka kamu a jihar Zamfara.
Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara, Dr Aisha M.Z. Anka ya tabbatar da bullar Sabuwar cutarda ba a san ta ba a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Ibrahim Bello Boko ya raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.
Sanarwar ta ce rashin lafiyar na da nasaba da kumburin ciki, kara girman hanta da mafari, zazzabi da raunin jiki
Sanarwar ta kara da cewa, “An fi samun barkewar cutar a kananan hukumomin Maradun, Shinkafi da Gusau a jihar”.
“Yara sun fi fama da cutar kuma ana danganta cutar da shan ruwa”
“Ya zuwa yanzu, an gano kimanin mutane dari da saba’in da bakwai (177) kuma an samu rahoton mutuwar mutane 4.”
“An kai rahoton faruwar lamarin ga Hukumar NCDC da duk masu ruwa da tsaki.”
Haka zalika “Samfurin halittu daban-daban na mutane da na dabbobi, samfuran ƙasa, samfuran ruwa, samfuran n kayan abinci an kai su dakunan gwaje-gwajen Legas da Abuja don yin nazari. Kamar yanda Jaridar Daily Post ta ruwaito
“Ma’aikatar za ta ci gaba da sabunta jama’a da duk abokan huldar da suka dace kan duk wani sabon binciken da aka samu da wuri.”
