News
Gwamnatin Zamfara Ta Karyata Rahoton Hukuncin Kisa Kan Zargin Ridda
Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa, musamman Sahara Reporters, da ke cewa wata mata mai suna Zainab Muhammadu na fuskantar hukuncin kisa a jihar saboda sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa babu irin wannan shari’a da ke gudana a kowace kotu a jihar, musamman kotun shari’ar Musulunci.
Kashi 2.5% Kacal Na ‘Yan Najeriya Ke Kula Da Matsalar Hawan Jini – NHS
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan wani kazamin rahoton karya da ke yawo a kafafen yada labarai, wanda ke cewa wai wata matashiya mai suna Zainab Muhammadu, mai shekaru 22, na fuskantar hukuncin kisa saboda ta koma addinin Kirista,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin “makirci daga wasu gurbatattun mutane da ke neman tayar da zaune tsaye da kawo fitina a jihar,” tana mai jaddada cewa babu wani sahihin bayani da ke nuna an kama ko kuma ake shari’a da wata Zainab kan zargin ridda.
Har ila yau, gwamnatin ta ce ta tuntubi hukumomin tsaro da na shari’a domin tantance gaskiyar lamarin, kuma an tabbatar da cewa rahoton karya ne daga tushe.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta ce hoton da aka danganta da Zainab Muhammadu a cikin rahoton Sahara Reporters na wata mata ce daban mai suna Aslia, wadda ke zaune a Texas, Amurka.
Gwamnatin ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka kirkiri labarin da kuma daukar matakin doka a kansu.
“Ba za mu lamunci yunkurin tayar da hankali a tsakanin al’umma ba, musamman ta hanyar yada labaran karya da suka saba da gaskiya da kwanciyar hankali na jama’a,” in ji gwamnatin jihar.
