Connect with us

News

Kotu Ta Samu Awakan Da Gwamantin Kano Ta Gurfanar Gabatanta Da Laifi Dumu-dumu

Published

on

Wata kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin daurin wata guda a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 25 ga wasu mutane da ke da mallakar awaki 17, bayan samun su da laifin lalata shuke-shuken gwamnati da barnatar da dukiyar al’umma.

An gurfanar da mutanen a gaban kotun ne bisa zargin barin dabbobinsu su ci da lalata shuke-shuken da gwamnatin jihar ta dasa a kan titunan Lodge Road da Race Course a cikin birnin Kano.

Advertisement

Kotu Ta Samu Awakan Da Gwamantin Kano Ta Gurfanar Gabatanta Da Laifi Dumu-dumu

Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano ce ta shigar da karar, inda ta zargi masu awakin da saba dokar kula da lafiyar muhalli da kare shuke-shuke.

Mai shari’a, Barrister Bahijjah H. Aliyu, ta yanke hukunci bisa sashi na 7 (e) na Kundin Dokokin Kula da Lafiyar Al’umma na shekarar 2019, inda ta samu su da laifi.

Advertisement

Kotun ta ba da zaɓi ga kowane mai dabbobin ko ya zauna a gidan gyaran hali na tsawon wata guda, ko kuma ya biya tarar naira dubu 25. Baya ga haka, an umarce su da su biya naira dubu 100 kowanne a matsayin diyya kan barnar da awakin suka yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending