Connect with us

News

Bunkasa Harkar Kasuwanci  Shine Kashin Bayan Cigaban Tattalin arzikin jihar Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Mai girma Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf inda aka tattauna muhimman abubuwa musamman abun da ya shafi dokokin gwamnati, akan koyawa matasa Sana’o i da dabaru da zasu habbaka cigaban tattalin arzikin jihar kano baki daya.

Advertisement

Taron ya samu halattar manyan shuwagabanni daga bangarori da dama ciki harda Daraktoci da sauran wakilai daga dukkan bangarori da manyan yan kasuwa .

Jamhuriyar Nijar ta kori Amurka saboda barazanar takunkumi a kan Iran

Jamilu Abbas shine a matsayin wakilin Gwamnati mai bada shawara ta musamman akan al’amuran kasuwanci.

Advertisement

Jamilu Abbas ya shaidawa mahalarta taron mahimmancin bunkasa harkar kasuwanci wanda shine kashin bayan cigaban tattalin arzikin jihar. Ya kuma tabbatarwa al’ummar jihar Kano cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana iya bakin kokarinta wajen karawa al’umma kwarin gwiwa domin bunkasa harkokin kasuwanci.

Suma mahalarta taron sunyi tsokaci dangane da muhimmancin Gwamnati da irin rawar da take takawa domin bunkasa harkar kasuwanci, ciki harda sanya dokoki wadanda zasu bada yanayi mai kyau ga abokan kasuwanci wanda zai karfafa alaka tsakaninsu domin bunkasa tattalin arzikin jihar dama ciyar da ita gaba.

Advertisement

Yakara da cewa Gwamnatin Engr Abba Kabir Yusuf a shirye take domin sadaukar da lokutanta wajen kirkiro duk wani abu daka iya zama sila wajen samawa matasa abubuwan yi domin bunkasa Jihar Kano baki daya.

A karshe ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano tana sane da dukkan koken al’umma musamman abunda ya shafi hanyoyi, gine gine na zamani da kuma goyon bayan masana masu bada shawarwari akan al’amuran kasuwanci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending