Connect with us

News

Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Jihar Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yansanda ta NSCDC reshen jihar Kano ta dakile wani yunkurin fashi a Unguwar Fulani da ke karamar hukumar Kumbotso bayan amsa kiran gaggawa.

Advertisement

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar a jihar, SC Ibrahim Abdullahi, ya fitar, ta bayyana cewa, amsa kiran gaggawa da jami’an NSCDC daga ofishin Kumbotso suka yi, ya kai ga kama wasu mutane 9 da ake zargi da hannu a yunkurin fashin da aka dakile.

Kungiyar  ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki A Kasa Baki Daya

Wadanda ake zargin, sun hada da Abba Nasiru Adamu, Ibrahim Adamu, Hassan Sulaiman, Basiru Aliyu, Hashimu Ibrahim, Umar Hudu Hassan, Shamsu Haruna, Ibrahim Abubakar, da Mudassir Hassan Dahiru.

Advertisement

SC Abdullahi ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun shirya yin fashin ne a wani kamfani da ke cikin Unguwar masana’anta ta Challawa a jihar.

 

Advertisement

Leadership

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending