News
Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki A Kasa Baki Daya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya, ASUU, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a yayin da take kokawa kan gazawar gwamnatin tarayya ta nada majalissar gudanarwar jami’o’in tarayya.
Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya yi wannan barazanar a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Abuja.
TURNUƘU DAGA RIBAS: Gwamna Fubara ya ce zai binciki gwamnatin Nyesom Wike
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Kungiyar wacce ta ce gwamnatin tarayya ta rusa shugabannin jami’o’in a watan Mayun shekarar da ta gabata, ta bukaci ‘yan Najeriya da su dora wa gwamnati alhakin duk wani matakin da za ta dauka na nuna rashin amincewa da matakin da gwamnati ta dauka.
Advertisements
