News
TURNUƘU DAGA RIBAS: Gwamna Fubara ya ce zai binciki gwamnatin Nyesom Wike
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya sha alwashin binciken tsohuwar gwamnatin Nyesom Wike, yayin da ake cikin ƙazamin rikicin siyasa a jihar.
Fubara ya bayyana haka a ranar Litinin, lokacin da yake rantsar da Dagogo Iboroma, wanda ya naɗa sabon Antoni Janar, kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Ribas.
Hukumar Hisbah Ta Kama Matasa Maza Da Mata Su 20 Saboda Suna Wanka Tare A Kano
Haka wata sanarwar manema labarai ta ƙunsa, wadda Nelson Chukwudi, Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Fubara ya fitar mai ɗauke da sa hannun sa.
Iborama wanda babban lauya ne wato SAN, ya maye gurbin Kwamishinan Shari’a Zachaeus Adangor, makusancin Wike, wanda a cikin fushi ya yi murabus cikin Afrilu, bayan sauya masa ma’aikata, zuwa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
Tun cikin 2023 ne Jihar Ribas mai arzikin ɗanyen mai ta afka cikin rikicin siyasa, bayan ‘yan Majalisa masu goyon bayan Wike, sun ƙulla tuggun yunƙurin tsige Gwamna Fubara.
‘Za Mu Kafa Kwamitin Binciken Gwamnatin Wike’ – Gwamna Fubara:
Gwamna Fubara ya ce zai kafa kwamitin binciken irin gadangarƙamar da gwamnatin da ya gada ta tafka tsawon shekaru takwas a Jihar Ribase.
Premium Times ta ruwaito cewa Fubara ya naɗa sabon kwamishinan a daidai lokacin buƙatar hakan, domin akwai shari’u masu yawan gaske da ke buƙatar kammala su, amma sai an yi da gaske sosai.
“Da fatan za ka yi aikin ka sosai da sosai.”
“Kuma babban aikin ka shi ne zamu kafa kwamitin binciken yadda aka gudanar da gwamnatin da na hada. Kuma ba zan janye daga yin wannan bincike ba.
“Mun san za ka kare wannan gwamnati, saboda tarihin ayyukan ka ya nuna cewa ba ka da wata ƙazanta a jikin ka. Irin ka ‘yan baiwa ne, su na da tsoron Allah.”
Fubara ya nuna rashin jin daɗin cewa duk da cewa akwai matsalar ruɗanin siyasa a jihar, wanda kamata ya yi a ce an kawar da shi, sai ya ce abin takaici babu wata hanyar sasanta lamarin.
Ya ce yanzu ya na farin ciki saboda akwai halastacciyar majalisa a jihar, wadda za ta riƙa gudanar da aikin ta.
“Da na akwai dalilin da ya sa na ke haƙuri, ai saboda mu duk ‘yan gida ɗaya ne, rigimar cikin gida ce.
“To amma yanzu ta fito fili cewa maganar sasanci ba zai taɓa yiwuwa ba. Saboda tabbas akwai hujjoji masu nuna cewa akwai ƙoƙarin yi wa wannan gwamnati zagon ƙasa.
Fubara ya ragargaji tsohon Kwamishinan Shari’a wanda ya sauka. Ya ce ya na kwamishina amma ya riƙa yi wa gwamnatin sa zagon ƙasa.
