News
Matashi Ya Banka Wuta A Masallaci Ana Tsaka Da Sallah A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masallata da dama ne suka kone bayan wani matashi da har ya zuwa yanzu ba a gano wane ne ba ya yi amfani da fetur ya banka wuta a wani masallaci a Kano ana tsaka da Sallar Asuba.
Lamarin ya auku ne a kauyen Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Ko da ya zo ana tsaka da sallah sai ya kulle dukkanin kofofin masallacin, inda kafin masallatan su farga ya watsa fetur sannan ya cinna wuta ya tsere kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa Aminiya.
Kafin mutanen waje su ankara su kawo masu dauki kimanin mutum 20 sun kone kuma take aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano.
Advertisements
