News
Wasu ‘Yan bindiga sun harbi Firaministan Slovakia
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ‘yan bindiga dadi sun harbi Firaministan kasar Robert Fico, rahotanni sun ce an harbe Mr. Fico ne jim kadan bayan kammala wani taron majalisar ministoci a birnin Handlova da ke tsakiyar kasar.
Jaridar Dennik N daily, wacce wakilinta ya ga yadda jami’an tsaro suka dauke firayim minista a cikin mota, ya ruwaito cewa ‘yan sanda sun tsare dan bindigar da ake zargi, kuma tuni aka garzaya da shi asibiti.
Kungiyar Kwadago Ta NLC Yi Fatali Da Tayin Naira Dubu 48 A Matsayin Mafi Karancin Albashi
A martaninta na farko game da harbin, Shugabar gwamnatin Slovakia mai barin gado Zuzana Caputova ta bayyana kaduwarta matuka da harin da ta kwatanta da “rashin tausayi”.
Mista Fico ya koma kan karagar mulki a Slovakia bayan zabe a watan Satumban shekarar 2024, a karkashin wani kawancen masu ra’ayin kishin kasa.
