Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Bawa Ministan Kuɗi Awanni 48 Ya Gabatar Da Sabon Tsarin Ƙarin Albashi 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban ƙasa Bola  Ahmad Tinubu ya umurci Ministan Kuɗi, Wale Edun, da ya fito da jaddawalin abunda za a buƙata game da sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwana biyu.

Advertisement

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, Shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati bayan zaman ganawa da tawagar ta yi da shugaban kasa Tinubu a Fadar sa yau Talata.

Hukumar Kula Da Aikin ‘Yan Sanda Ta Saki Jerin Sunayen Kuratan Ƴan Sanda Dubu 10,000 Da Aka Ɗauka Aiki 

Cikin Mako guda an ba wa Dukkanin ɓangarorin da aka yi zaman tattaunawa da su kan sabon mafi ƙarancin albashi za su haɗu da kungiyoyin ƙwadago domin ganin an gabatar da sabon albashi ga ƴan Najeriya

Advertisement

“Za mu haɗu mu yi aiki ba ɓata lokaci na tsawon mako guda don tabbatar da cewa mun sami sabon albashi ga ƴan Najeriya wanda zai dawwama kuma mai inganci.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending