Connect with us

News

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace  Malaman Jami’a A Jihar Katsina

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Yan bindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza.

Advertisement

Leadership ta rawaito cewa, an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon.

Shugaba Tinubu Ya Bawa Ministan Kuɗi Awanni 48 Ya Gabatar Da Sabon Tsarin Ƙarin Albashi 

 

Advertisement

Rahotanni sun bayyana lamarin ya faru ne a GRA Dustin-Ma da misalin karfe 1:am na ranar Litinin.

An kuma rawaito cewa, ‘yan ta’addar sun afka GRAn ne da muggan makamai inda suka rika harbe-harbe a sama.

Advertisement

Da aka tuntubi Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai, ya ce, rundunar tana aiki tare da hadin guiwar sauran jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending