Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: Wale Edun Ya Mika Wa Shugaba Tinubu Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata 

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA 

Biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaban sabon tsarin mafi karancin albashin.

Advertisement

Sanarwar na zuwa ne kwanaki biyu bayan Tinubu ya bayar da umarnin gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi da kuma nazarin abin da ke tattare da shi.

Hajjin 2024: Jami’an Hukumar NDLEA Ta Kama Alhazai Da Ke Ta’ammali Da Kwayoyi

Rahoton na ministan kudi an ce zai zayyana wasu sabbin matakan mafi karancin albashi tare da tasirin kasafin ga gwamnatin tarayya.

Advertisement

Idan ba a manta ba Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa kungiyar kwadago ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a Litinin, domin neman karin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati.

Leadership ta ruwaito cewa a  gefe guda kuma ma’aikatan na bukatar janye karin kudin wutan lantarki da aka yi a baya-bayan nan.

Advertisement

Shugabannin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC, sun dakatar da aikin na tsawon kwanaki biyar bayan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin ci gaba da tattaunawa, tare da nemo sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending