Connect with us

News

Yadda wani mai gidan haya ya sheka lahira yayin musu da ɗan haya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wani mai gidan haya mai suna Benjamin Apeh ya yanke jiki ya fadi yayin da yake musu da wani ɗan haya saboda ƙin biyan shi kuɗin haya.

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Omolola Odutola ya ce lamarin ya auku ne a kauyen Arigbabu dake karamar hukumar Sagamu.

Abubuwa 7 Game Dokar Ta Ɓacin Ilimi Da  Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya Kafa

Odutola ya ce rundunar ta samu labarin mutuwar Apeh bayan ‘yar sa Precious ta kawo ƙara ofishin ƴan sandan.

Advertisement

Ya ce Precious ta faɗi wa ƴan sanda cewa mahaifinta da ɗan hayan sun kwana su taf musu a tsakanin su saboda kuɗin haya da ɗan hayan bai biya ba.

Ɗan hayan mai suna Apeh ya yi barazanar kashe mai gidan hayan a duk lokacin da suka bɓarke da gaddama.

Advertisement

“Precious ta ce mahaifinta ya yanke jiki ya faɗi bayan sun takaddamar da tashiga tsakanin shi da ɗan hayan yaki ƙarewa.

Premium Times ta ruwaito cewa Odutola ya ce rundunar ta fara farautar dan hayan domin kuwa bayan ya tabbata maigidansa ya mutu sai ya tattara ya arce.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending