News
Daruruwan Mutane Sun Banka Wa Wani Mutum Wuta Bisa Batanci Ga Al-Qur’ani
DAG A YAASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wasu fusatattun mutane a Pakistan sun kutsa kai cikin ofishin ‘yan sanda domin kwace wani dan yawon bude ido wanda daga bisani suka lakada masa duka har lahira kafin su banka wa gawarsa wuta bisa zarginsa da cewa ya yi Batanci ga Al-Qur’ani mai tsarki .
Mutumin mai suna Mohammad Ismail, dan yawon bude ido ne da ya ke zama a wani otel da ke garin, sai wasu gungun jama’ar garin suka kai masa hari tare da zargin shi da aikata sabo.
Yanzu Haka Matasan Da Suke Fadan Daba A Unguwar Ja,een Sun Kulle Hanyar Gaba Daya
Haka zalika sun kuma kona ofishin ‘yan sandan da ke garin Madyan a lardin Khyber Pakhtunkhwa, tare da kona motocin ‘yan sandan da ke wurin, a cewar jami’an ‘yan sandan yankin.
AL JAZEERA ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun yi rajistar wasu daruruwan mutane, kuma suna kokarin zakulo wadanda ke da hannu wajen kai hari a Ofishin ‘yan sandan tare da kashe mutumin.
Jami’in ‘yan sanda Rahim Ullah ya ce jami’ansu sun kai mutumin ofishin ne domin ba shi kariya amma jama’a sun mamaye ofishin da yawan gaske suka fatattake su.
Daruruwan mutanen unguwa ne suka fusata suka afkawa Ofishin ‘yan sandan, suka kwace Ismail, suka yi masa dukan tsiya wanda ya Kai ga Mutuwar sa har lahira, sannan suka kona gawarsa suka bar ta a hanya.
Karin jami’an ‘yan sanda sun isa Madyan domin shawo kan lamarin, in ji Mr Ullah.
An bayyana wanda aka kashe a kafafen yada labarai na cikin gida a matsayin dan yawon bude ido daga yankin Sialkot, Punjab.
