Connect with us

News

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe ofisoshinsa a faɗin Nijeriya daga 30 ga Yuli

Published

on

DAGA UASIR SANI ABDULLAHI 

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe duka ofisoshinsa da ke faɗin Nijeriya.

Advertisement

MTN ɗin ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter, amma bai sanar da ranar da zai sake buɗe su ba.

Matan Da Su Kan Yi Barci A Makare Sun Fi Saurin Kamuwa Da Ciwon Sukari

Wannan na zuwa ne bayan wasu fusatattun masu amfani da layin na MTN sun kai hari ga ɗaya daga cikin ofisoshin kamfanin a Legas a ranar Litinin.

Advertisement

A wani bidiyo wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Litinin, an ga wasu fusatattun mutane suna ƙoƙarin kada katangar ƙarfe da ke wajen ofishin na MTN.

Rahotanni sun ce waɗanda suka far wa ofishin na MTN sun aikata haka ne bayan an toshe musu layinsu sakamakon cikas da ke da akwai tsakanin layin nasu na MTN da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN.

Advertisement

MTN ɗin ya ce duk da ya rufe ofisoshin nasa, amma za a iya tuntuɓar ma’aikatansa ta wasu hanyoyin sadarwa.

Haka kuma rufe ofisoshin na MTN na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin soma zanga-zangar da ake tunanin za a yi a Nijeriya a ranar 1 ga watan Agusta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending