News
An samu jagoran zanga zangar matsin rayuwa a unguwar tudun Yola dake Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jagoran masu zanga-zanga a nan Kano a unguwar tudun yola Auwal Baban Jimaga ya ce zanga-zanga babu gudu babu ja da baya, har sai gwamnatin tarayya ta biya musu muradansu.
Kwamared Auwal ya ce komai ya lalace a kasar nan talaka na fama da matsaloli masu yawa wanda su shugabanni basu damu da halin da talakawa ke ciki ba.
Ta cikin tattaunawar da aka yi dashi Auwal ya ce kayan masarufi sunyi tsada abinci ya fi karfin talaka, talakawa na kwana ba bu cin yau bare na gobe wanda hakanne ke kara haifar da damuwa da Kuma cutar da rayukan su
Ya kara da cewa sanin kowa ne bangaren lafiya da ilimi da sauran bangarori babu wani cigaba sai ko ma baya.
Ya Kuma ce matukar Gwamnati naso su janye zanga-zangar da suka shirya to dole ne su cika wadannan abubuwa kamar haka.
Jaridar inda ranka ta rawaito A Ranar 1 ga watan Augusta ne za’a fara gudanar da zanga-zanga dan kyamatar yunwa a fadin kasar
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
