News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Sassauta Dokar Hana Zirga Zirga Da Ta Sanya Sakamakon Ayyukan Bata Gari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga zirga da ta sanya sakamakon ayyukan bata gari da sunan zanga-zanga, za’a dinga fita daga karfe takwas na safe zuwa biyu na Rana.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Baba Halilu Ɗan Tiye, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa da Jaridar INDA RANKA, a daren Asabar 03 ga watan Yulin 2024, ya ce an sassauta dokar ne domin al’umma su fito su gudanar da harkokin su na yau da kullum, bisa damuwar da aka shiga.
Ya ci gaba da cewa, yanzu mutane suna da damar da zasu fito su gudanar da al’amuran su kamar yadda aka saba a baya, yana mai cewa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya damu matuƙar gaske kan yadda al’ummar jihar suka samu kan su a ciki.
“Gwmanatin jihar Kano tana kuma ƙara jajanta wa al’ummar jihar musamman wadanda suka yi asarar dukiyoyin su yayin zanga-zangar lumanar tsadar rayuwa, yana kuma addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su, ya bai wa iyalan su haƙuri, “in ji Kwamishinan”.
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fitar ne da yammacin ranar Alhamis 01 ga watan Agustan 2024, bayan da wasu daga cikin matasa suka rikiɗar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, zuwa fasa shagunan mutane tare da ɗibar musu kayayyaki da kuma na gwamnati har da barnar wa.
wasu matasa ne dai suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana akan tsadar rayuwa, da matsalar tsaro a ƙasar nan, domin nusartar da gwamnatin tarayya halin da aka samu kai a ciki, al’amarin da zanga-zangar ta ƙazanta a wasu guraren.