News
Da Dumi-Dumi Tinubu zai yi wa Yan kasa jawabi a gobe Lahadi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi wa Yan kasa jawabi a gobe Lahadi 04/08/2024 da misalin karfe 7am na safe agogon Nijeriya
Rahotanni dai na nuni da cewa Shugaban kasar zai yiwa Al, ummar nageriya bayani Kan matsayar sa gameda koken da Yan Nigeria ke ciki na kuncin rayuwa duk sabida cire tallafin man fetur
Tashoshin yada Labarai na kasa NTA da Rediyon Tarayya FRCN da wasu daga cikin shafukan sadarwa zasu yada jawaban Shugaban
Baya ga hakan zaa maimaita jawabin Shugaban da yammacin Lahadin da misalin karfe 3 na rana
Wannan ya biyo bayan Rikita-Rikitar Zanga-Zanga da yau take cika yini na uku da farawa da aka soma tun Alhamis din makon jiya da manufar gargadar Gwamnatin kan halin tsadar rayuwa da matsi da matsalar tsaro.
Kafin yanzu babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta soki Shugaban da kame baki duk da rikidewar da Zanga-Zangar tayi zuwa sace sace da kashe kashe.
Details soon
-
News7 days ago
HAWAN DABA DA KILISA :Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Za Ta Lamunci Kalaman Tada Zaune Tsaye Ba
-
News7 days ago
An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto
-
News5 days ago
Kwankwaso Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Marawa Sauye-Sauyen Shugaba Tinubu Baya
