News
Kano :Ana Fargabar Mutuwar Masu Zanga Zanga Da Dama A Unguwar Kurna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Duk da dokar hana fita ta awanni 24 a jihar Kano, Masu zanga zanga a jihar sun zargi jami’an tsaro da harbi kan masu zanga zanga a Unguwar Kurna yau Asabar.
Ta cikin wata ganawa da jaridar INDA RANKA ta yi wani mazaunin yankin kuma guda cikin masu zanga zangar Kwamared Usman Bandiro. yace sun fito zanga-zangar ta lumana amma wasu cikin jami’an ‘yan sandan dake aiki domin samar da tsaro suka fara harba musu hayaki mai saka hawaye inda daga bisani kuma suka fara harbin su da bindiga.
Kaso 75 Cikin 100 Na Yan Arewacin Yan Najeriya Basa Iya Cin Abinci Sau Uku A Rana —Gwamna Uba Sani
Badirawo ya ce muddin aka cigaba da tafiya a haka baiga dalilin dazai saka su koma gida ba har sai gwamnati tayi musu abinda ya kamata, na dawo da tallafin man fetur da magance tsadar rayuwar a fadin Nijeriya.
Ana fargabar an harbi mutum sama da Goma cikin masu zanga-zangar
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zangar na dauke da kwalaye da aka rubuta korafe korafensu daban-daban.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar hana fita ta awanni 24 bayan bata gari sun kutsa cikin masu zanga-zanga.
-
News7 days ago
HAWAN DABA DA KILISA :Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Za Ta Lamunci Kalaman Tada Zaune Tsaye Ba
-
News7 days ago
An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto
-
News5 days ago
Kwankwaso Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Marawa Sauye-Sauyen Shugaba Tinubu Baya
