News
Kaso 75 Cikin 100 Na Yan Arewacin Yan Najeriya Basa Iya Cin Abinci Sau Uku A Rana —Gwamna Uba Sani
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya bukaci dukkanin shuwagabannin arewa da suji tsoran Allah akan nauyin da kuma alkawarin da suka dauka na kare dukkannin al,ummar su.
Uba sani ya bayyana hakanne a lokacin da yake amsa tambayoyin sashin Hausa na BBC akan yadda zanga zanga take gudana a Jihar Kaduna
Gwamnan yace Tabbas jahohin arewa muna cikin yunwa da fatara da Kuma kakani kayi kuma tabbas tun shekaru goma sha biyar yakamata ace shugabannin arewa sun maida a hankalinsu akai tare da magance wannan matsaloli.
Uba Sani ya ce a shekarun Baya jahohin arewa basa fuskantar irin wadannan matsalolin na rashin tsaro talaucin da kashe kashen al,umma musamman ma jahohin arewa maso yamma amman yanzu suma sunshiga jirin jahohin da ke fama da tashe tashen hankula sabida san zuciya irin na shuwagabannin mu
Haka zalika nima banbcire kaina daga jerin irin wadannan shuwagabanni sabida Nima idan za,ayi gyran dole dani za,ayi sabida nauyin alkawarin Shugabancin dake wuya na
gwamnan yace tabbas Kaso 75 cikin 100 na Yan arewacin yan Nigeria Suna cikin wani hali Kuma basa iya cin abinci sau uku a duk rana
Koda aka yimasa tambaya akan zanga zanga da jama,a suka fara gudanarwa a ranar 1 Augusta gwamnan ya goyi da bayan hakan inda yace doka ce ta baiwa kowa dan kasa damar yin hakan Kuma hakan ne kawai zai nunawa shugabanni irin matsalolin da al, ummar su take ciki .
Gwamnan Sani ya ce Kuma a matsayain mu a jagororin siyasa dole ne mu girmama wannan doka amman muma zamuyi yan dabaru wajen ganin anyi zanga zangar cikin kwanciyar hankalin da lumana
Kafin a fara gudanar da zanga zangar Saida muka zauna da masu ruwa da tsaki na gwamnati mun kuma shawarci jamia,n tsaro akan subi Jama,ar mu a hankali yayin da suke gudanar da zanga zangar lumana.
Gwamnan yace bazamu hana Jama,a yin zanga zanga ba amman ba,a bata gari a cikin su Kuma Koda munsami irin wadan na zamubi irin Sahun irin kasashen da suka fimu cigaba wajen girmama dumukradiyya idan aka sami bata gari a cikin masuyin zanga zangar anabinsu ne da hayaki maisa hawaye ko Kuma fesa musu ruwan zabi
Gwamnan ya ce wannan shawarwari da suka bayar sunyiwa jami,an tsaron tasiri domin kuwa babu rashin rai na ko mutun daya da akayi a Jahar Kaduna
