News
Zanga-Zanga: Yakamata shugaban ƙasa ya yiwa ƴan Najeriya cikakken jawabi – CUPP
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gamayyar jam’iyyun siyasa ta CUPP ta caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan abinda ta bayyana da ɗabi’ar ko-in-kula game da zanga zangar da ake yi game da tsadar rayuwa.
Gamayyar ƙungiyoyin sun bayyana tsarin shugabancin Tinubu a matsayin mafi muni wanda ya jefa kasar nan cikin mummunan hali.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gamayyar jam’iyyun, Mark Adebayo, ƙungiyar ta ce maimakon shugaba Tinubu yayiwa yan kasa jawabi kai tsaye sai ya bari makusantansa na bayanai na fusata yan Najeriya.
Sanarwar ta ce “A yayin da ake yin zanga-zanga a fadin kasa, shugaban kasa yana ganin ba zai iya yiwa yan kasa jawabi kai tsaye ba. Sai dai ya zabi sanya jami’ansa na kalaman fusata yan Najeriya”.
Jam’iyyun sun ce kamata yayi shugaban kasar yayiwa ƴan Najeriya jawabi tare da sassautawa al’umma.
PUNCH
