News
Gargadi Ga Wadanda Ke Karatu A Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha (Polytechnic) Daga Hukumar NYSC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) ta yi gargadin cewa wadanda suka kammala karatu a Kwalejojin kimiyya da fasaha ba tare da shaidar kammala horo na shekara daya (IT) ba ba za a tura su aikin yi wa kasa hidima ba.
Yetunde Baderinwa, Ko’odinetan NYSC a Jihar Legas ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Asabar a Legas.
Baderinwa ta ce hukumar NYSC ta fitar da sanarwa a kan hakan.
Baderinwa ta ce: “An lura cewa wasu dalibai da ke karatu a kwalejojin kimiyya da fasaha ba sa kiyaye wajabcin yin aikin horo na IT na shekara daya kafinsu dawo kammala karatun su na HND.
“Dole sai mutum ya yi shekara daya na horo, wato IT shine sharadi na HND.
“Dole ne su yi aikin IT na shekara guda tare da shaidar kammala karatunsu kafin su tafi HND, kuma dole ne hukumomi su tabbatar da hakan kafin a shigar da su HND.
Duk wanda ba shi da wannan shaida ba za a tura shi aikin bautar kasa ba.
