Connect with us

News

Ya Zama Dole Gwamnati Ta Samar Wa Matatar Man Dangote Ɗanyan Man Da Za Tayi Amfani – Ƙungiyar lauyoyin Najeriya

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ƙungiyar lauyoyin Najeriya ta gargadi gwamnatin ƙasar da kar ta kuskura ta bari matatar man dangote ta durƙushe saboda rashin samun ɗanyan man da za tayi amfani da shi wajen gudanar da ayyukanta.

Shugaban ƙungiyar mai barin gado Yakubu Mai Kyau ya ce abin baƙin ciki ne yadda Dangote ke fuskantar zagon ƙasa daga bangarori da dama wajen ganin matatar ta fara aiki gadan gadan.

Yara Fiye Da Miliyan Hudu Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa A Arewacin Najeriya  – Gwamnatin Tarayya

Mai Kyau ya zargi masu shigo da mai ƙasar waɗanda suka hana Najeriya tace mai a gida da haifar da tarnakin da ya hana sabuwar matatar aikin tace man da zai hana ƙasar shigo da shi daga ƙasashen ƙetare.

Shugaban wanda ya jagoranci tawagar muƙarrabansa domin ziyarar gani da a ido matatar dake unguwar Lekki a Lagos, ya ce abinda ya gani ya faranta masa rai matuka, yayin da ya bayyana Aliko Dangote a matsayin mai fafutukar ƴantar da jama’a kuma gwarzo saboda sadaukar da ran da ya yi wajen zuba jarin dala biliyan 20 domin samar da matatar.

Mai Kyau ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta samar da yanayi mai kyau ta yadda wannan matatar zata fara aiki gadan gadan domin ragewa Najeriya wahalar da ta ke sha na samun tacaccen man.

Advertisement

 

FRI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending