News
Yara Fiye Da Miliyan Hudu Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa A Arewacin Najeriya – Gwamnatin Tarayya
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa kananan yara fiye da miliyan hudu ne su ke cikin halin matsananciyar yunwa sakamakon rashin samun abinci mai gina jiki a a Arewacin Najeriya.
Ladidi Bako-Aiyebusi, darakta mai kula da bangaren kimiyyar abinci a ma’aikatar lafiya da walwala, ita ce ta bayyana hakan ranar Laraba yayin wani taro da kwararru a bangaren kimiyyar abinci wanda aka kaddamar ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar Nasarawa da ke Keffi Jihar.
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Buƙaci Al’umma Su Kare Kansu Daga Hare-haren ‘Yan Bindiga
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ma’aikatar lafiya ta shirya taron ne domin hada gwuiwa da ma su ruwa da tsaki da kuma kwararru domin samar da wani tartibin tsari na samar da abinci a Najeriya.
Taron, wanda aka fara ranar Laraba, ana sa ran kammala shi a ranar Asabar.
Mahalarta taron sun hada da kwararru a bangaren kimiyyar abinci, Malaman manyan makarantu, kungiyoyin hidimtawa jama’a da sauran su.
A jawabinta na bude taro, Ladidi ta bayyana cewa taron zai samar da wata manhaja da za ta zama linzami wajen warware matsalolin da suka shafi samar da abinci mai gina jiki a Najeriya
Ta bayyana cewa a halin yanzu Najeriya na fuskantar tsananin halin rashin samun abinci mai gina jiki wanda hakan ya shafi lafiyar jama’a da samun cigaban kasa.
A cewar Ladidi, wani bincike a kan cimaka da aka gudanar a shekarar 2021 ya nuna cewa akwai kananan yara kusan miliyan 4.4 a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma da suke fama da tsananin yunwa.
“Abubuwan da aka gano sun haddasa wannan matsala sun hada da karancin abinci, rashin cin abinci mai gina jiki, talauci, rashin ilimi da sauran su,” a cewar ta.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
