Connect with us

News

Tashin Farashin Man Fetur Ya Haifar Da  Matsalar Sufuri A Jihar Kano   

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ana samun hauhawar farashin man fetur a jihar Kano, lamarin da ya haifar da tashin farashin ababan hawa a tsakanin mazauna jihar.

Rahotanni na nuni da cewa an rufe wasu gidajen mai, yayin da wadanda suka rage a bude suke sayar da man Fetur a farashi mai tsada, daga N950 zuwa N1200 zuwa sama, lamarin da ke kara tabarbare a jihar.

Advertisement

Badamasi, wani direban A daidaita sahu daga Dorayi, ya bayyana kokawarsa da hauhawar farashin man fetur.

Ya bayyana cewa a yanzu yana biyan N950 zuwa N970 a kowace lita a gidajen masu zaman kansu, idan aka kwatanta da N620 da yake biya a gidajen mai na NNPC, wanda a yanzu ya kai Naira 897 a kowace lita.

A cewarsa, hakan ya shafi sana’arsa ta Adaidai ta sahu , inda a wasu lokuta yakan dauki kasa da adadin da ya kamata ya karba “Duk da sayen man da ya yi tsada, ba mu kara kudin sufuri sosai ba, amma har yanzu wasu fasinjojin na zargin mu da yunkurin yin magudi kan lamarin. Ko kuma sun ki shiga abin hawan  mu.”

Advertisement

Wata dalibar Polytechnic ta jihar Kano, Salama Ibrahim ta koka da yadda farashin sufuri daga makaranta zuwa gida ya tashi daga N200 zuwa N300-N350. Ta bayyana dabarun da take bi, tana mai cewa, “Don in sami kuɗi, wasu lokuta nakan yi tattaki daga makaranta zuwa Kabuga sannan in ɗauki keke daga can zuwa gidana, saboda farashin kuɗin  yana da tsada sosai.”

Haka lamarin ya shafi ‘yan kasuwa. Abdulsamad Isiyaku, dan kasuwa, ya bayyana cewa tsadar man fetur na kara tsadar kayan masarufi, wanda a karshe yake fargabar zai yi wa kwastomominsa nauyi. “Mun gaji da wahala ,” in ji shi.

“Muna kira ga Shugaba Tinubu da ya taimaka mana ta hanyar rage tsadar man fetur, saboda tsadar kayayyaki ya shafi komai kuma yana kawo mana wahala.”

Advertisement

A baya-bayan nan ne dai Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya kara farashin famfunan man fetur daga Naira 617 zuwa Naira 897 kan kowace lita, inda ya ce bashin da ya haura dala biliyan 6 ya kai ga farashin man fetur.

Wannan bashi ya shafi dorewar samar da man fetur, wanda ya haifar da karancin man da ke kawo cikas a rayuwar yau da kullum a Kano.

Yayin da Lamarin ke kara ta’azzara, mazauna yankin na ci gaba da yin kira ga gwamnati da ta gaggauta shiga tsakani domin rage musu radadi

Advertisement

 

 

 

Advertisement

Daily News24

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *