Connect with us

News

Dole Ne Shugaba Kasa Ya Umarci Kamfanin NNPCL Ya Janye Karin Farashin Man Fetur _ Kungiyar SERAP

Published

on

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da ”matsayinsa ya tilasta wa babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da ƙungiyar ta kira ‘wanda ya saɓa wa doka.

Advertisement

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da dokokin ƙasa game da kare hakkin Dan Adam.

SERAP ta kuma buƙaci shugaba Tinubu ya ”umarci babban lauyan gwamnatin ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki zarge-zargen cin hanci da almabazzaranci da ake yi wa kamfanin NNPCL.

Advertisement

Ciki har da kuɗin tallafin ƙwatar kai (bailout), na dala miliyan 300 da kamfanin ya karɓa daga gwamnatin tarayya a watan Agustan da ya gabata, da kuma zargin kamfanin da rashin saka ribar mai a asusun gwamnati.

SERAP ta ce “ya kamata a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a NNPCL a gaban kotu domin su fuskanci hukunci, idan har an same su da laifi, tare da ƙwato duk abin da suka sata”.

Advertisement

ƙungiyar ta kara da cewa cin hanci da rashawa da ake zargin samu a fannin man fetur da kuma kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙai’da ba, da kuma yin ƙunbiya-ƙunbiya ko rufa-rufa sun taimaka wajen ƙarin taɓarɓarewar al’amura a kamfanin, wanda kuma shi ke haifar da ƙarin kuɗin man fetur a koyaushe a ƙasar.

Al, ummar Nageriya dai na cikin wani mawuyacin hali tun kafin Kamfanin mai na NNPCL  ya sanar da  Karin  farashin litar man Fetur din.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending