Business
Babban Bankin Najeriya CBN Ya Fara Sa Ido Kan Masu Sana’ar POS
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Babban bankin Najeriya CBN ya fara bin diddigin masu sana’ar POS, saboda hada-hadar takardar kudi na karkata musu maimakon bankuna, ciki har da kudin fansa bayan garkuwa da mutane.
Sannu a hankali, hada-hadar takardar kudi a Najeriya na karkata daga bankuna zuwa masu sana’ar POS. Sai dai, ana dada kallon karuwar karbar kudaden fansa sakamakon ayyukan ta’addanci da ke ta’azzara a halin yanzu. Abin da ya kai kasar ga fara mai da hankali zuwa kafar POS, tare da Babban Bankin Najeriyar da fitar da wata sabuwar sanarwar bin diddigin aiyyukan POS a Najeriya.
CBN ya umarci manyan kamfanonin da ke harkokin POS da su rika bai wa babban bankin bayanai a duk wata na daukacin hada-hadar kowane POS da ke Najeriya a halin yanzu.
Gwamnatin Tarayya na fatan bin diddigin kudaden fansa sakamakon ayyukan barayin daji da na birni da ke karuwa a cikin kafar POS.
Sai dai da kamar wuya kwalliyar babban bankin ta kai ga biyan kudin sabulu, a tunanin Dr Surajo Yakubu dake zaman kwarrare a laifukan kudi.
Kudi na taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar ayyukan ta’addanci a NajeriyaKudi na taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar ayyukan ta’addanci a Najeriya
Sama da POS miliyan biyu ne ke hada-hadar kudi a tudu da lungunan tarayyar Najeriyar. A bara kadai, kasar ta yi hada-hadar da ta kai ta sama da Tiriliyan 10 a cikin kafar POS, wannan na zama adadi mafi yawa kuma alamu na karuwar farin jinin kafar tsakanin al’umma.
Ana kallon POS a matsayin damar aiki da dubban daruruwa na ‘yan Najeriya da ke kare karatu ba tare da damar ayyuka a kasar ba, kamar matashi Nurrudeen Abubakar da ke sana‘ar POS bayan kare makaranta. A bara kadai, wata kididdigar da ba ta da tabbas ta ce an biya kudaden fansa da suka kai kusan Naira miliyan dubu 60 a jihar Sokoto ta POS, a daya daga cikin tunga ta ayyuka na barayin dajin. Sai dai a tunanin Kyaftain Abdullahi Bakoji da ke sharhi kan batun tsaron, an bar jaki ana dukan taiki.
Kungiyoyin ta’addanci na kai hare-hare da sace mutane don samun kudin fansaKungiyoyin ta’addanci na kai hare-hare da sace mutane don samun kudin fansa
Najeriya na a tsakanin habaka hanyar aikin miliyoyin matasan da ke zaman kashe wando, da kuma tinkarar rashin tsaron da ke da ruwa da tsaki da kudade na haramun.