Connect with us

News

Akalla Mutume 259 Ne Suka Mutu Yayin Da 625,239 Suka Rasa Matsugunansu A Ambaliyar Ruwa A Najeriya  – Hukumar NEMA

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce mutum 259 ne suka mutu yayin da wasu 625,239 suka rasa matsugunansu sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa a Najeriya a tsakanin watan Afrilu zuwa Satumban 2024.

Kazalika hukumar ta ce mutane 1,048,312 ne iftila’in ambaliyar ruwa  ya shafa a jihohi 29 da ƙananan hukumomi 172 a faɗin Najeriya, kamar yadda Darakta-Janar ta Hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar ta bayyana a cikin rahoton taron gaggawa na kasa  (ECF) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Advertisement

Kotu Ta Umarci A Tsare Magidanci Har Sai Ya Kammala Tunanin Yadda Zai Kula Da Iyalinsa

Shugabar ta jajanta wa waɗanda lamarin iftila’in ya shafa tare da su tabbacin cewa gwamnatin Tarayya karkashin hukumar NEMA za ta ba da dukkan tallafin da ya kamata kana ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan da suka dace.

A cewarta, makasuɗin kiran taron, shi ne don a samu bayanai kan lamarin ambaliyar Ruwa a Najeriya tare da bai wa masu ruwa da tsaki ayyukan da za su taka rawa akai.

Advertisement

Ta ce ana kan ƙoƙarin ganin an rage tasirinsa wahalhalun da yanayin ya haifar, duk kuwa da cewa ba za a iya daƙile aukuwar iftila’in ambaliyar gaba ɗaya ba.

”NEMA ta samar wa mutanen da suka rasa matsugunansu sansanoni a wasu jihohi tare da tura ƙarin ma’aikata don taimakawa a ayyukan bincike da ceto.

Advertisement

Haka kuma, hukumar ta samar da kayan aiki na tsaftace ruwa da aikin bincike da ceto ga jihohin da lamarin ya shafa,” in ji ta.

Ta kuma ya zuwa yanzu dai lamarin bai fi ƙarfin gwamnatin Najeriya ba.

Advertisement

A mummunan iftila’in  da ya afka wa jihar Borno kuwa sakamakon fashewar Madatsar Ruwa ta Alau, NEMA ta ce an fara samun janyewar ruwan a birnin Maiduguri, sannan al’amura na yau da kullum sun soma komawa daidai a babban birnin.

“Ba za mu ce mun kawo ƙarshen aikinmu ba, za mu ci gaba da ba da agajin gaggawa ba dare ba rana tare da sa ido da kuma tantance yanayin da ake ciki, don haka yana da muhimmanci ci gaba da bayyana yanayin da ake ciki.

Advertisement

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending