News
Ma’aurata Sun Mutu Sakamakon Hayakin Janareta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar ta tabbatar da mutuwar wani mai suna Nwachukwu Ikechukwu, bayan da ya shaka hayakin janareta a gidansu da ke unguwar Shogoye da ke Owode-Egba a cikin karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar.
An ce Ikechukwu da matarsa, Oyin Falodun, sun saka janareta a dakinsu da misalin karfe 10 na daren ranar Alhamis, amma wani makwabcinsa mai suna Oladayo Olasubomi, da ya zo ya ajiye Naira 1000 ga matar a kullum ya tarar da ma’auratan suna kwance.
Hukumar EFCC Na Ci Gaba Da Neman Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Ruwa A Jallo
Punch ta ruwaito cewa Olasubomi ya tayar da karar wanda ya ja hankalin wasu makwabta ciki har da shugaban kungiyar, wani Showunmi Sunday, wanda ya kai rahoton abin bakin ciki ga sashin Owode-Egba na rundunar ‘yan sandan jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai ranar Asabar.
Bayan da aka samu iskar wannan mummunan lamari, an ce jami’an ‘yan sandan sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka gano cewa babu wani tashin hankali a kan marigayin.
Odutola ya ce yayin da Ikechukwu ya rasa ransa a lamarin, matarsa da aka garzaya da ita asibiti daga baya ta farfado ta kuma bayyana abin da ya faru.
Ta kuma bayyana cewa daga baya ta gano cewa su biyun sun fado daga kan gadon da suke kwance kuma mijin nata ya yi ta faman tashi daga gadon bayan ya fadi.
Yayin da aka ce Falodun yana jinya a Asibitin Ore Ofe, Owode-Egba, an ce an ajiye gawar Ikechukwu a babban asibitin Owode-Egba domin a duba lafiyarsa.
