News
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata, Bayan Da Tankar Mai Ta Yi Bindiga A Abuja
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Fasinjoji da dama sun jikkata, bayan da wata tankar mai ta yi bindiga da yammacin Litinin a kan titin Shehu Shagari da ke yankin Maitama a Abuja.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:40 na yamma kusa da ginin ofishin Jakadancin Birtaniya.
Jami’an Hukumar EFCC Sun Gargaɗi Masu Amfani Da Kayan Aikinsu Suna Haɗa Bidiyon Barkwanci
Wani ganau, Saminu Sani, ya ce wutar da ta tashi yana kai wa tsayin hawa na huɗu na benen ginin Ofishin Jakadancin Birtaniya, lamarin da ya sanya direbobi barin motocinsu domin neman tsira.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya haddasa cunkoso mai yawan gaske a hanyoyi guda huɗu da ke haɗa Kasuwar Manoma, Otal ɗin Nicon Hilton, hedikwatar MTN, da kuma Chicken House.
Wani jami’in lafiya a Asibitin Maitama, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewar an kawo waɗanda suka jikkata don ba su agajin gaggawa.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira sun ce direban tankar ya tsere daga wajen jim kaɗan bayan tankar ta kife a ƙasa.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
