Connect with us

News

Mutane 5 sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa – ‘Yan sanda

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Rundunar ‘yan sandan ta ce manoma sun jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a dajin Hayin Kogi da ke karamar hukumar Birnin kudu a jihar Jigawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya fitar ranar Litinin.

Ko Majar Jam’iyyun Adawa Na Iya Kawo Karshen Mulkin APC A Najeriya  A Shakarar 2027?

“Rahoton da rundunar ta fitar ya nuna cewa a manoma da ke dajin Hayin Kogi sun far wa manoma mazauna kauyukan Waza Fulani na karamar hukumar Birninkudu a lokacin da suke aikin aikin noman damina.

PPRO ya kara da cewa da samun rahoton, ‘yan sandan da ke makwabtaka da shiyya ta ‘yan sanda, da ke kewaye da dajin, nan da nan aka tura wurin lamarin ya far.

Ya ce an kai wani mutum mai shekaru 42 da kuma wasu hudu da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Dutse inda aka yi musu magani

Advertisement

Ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kamo wadanda ake zargi akan lamarin, yayin da ake ci gaba da bincike .

“Tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya a yankin. Kwamishinan ‘yan sanda (CP), Mista Ahmadu Abdullahi, ya shirya taron masu ruwa da tsaki tare da bayar da umarnin cafke masu laifin.

CP ya umurci kwamandan yankin Birninku da jami’an ’yan sanda na yankin Birninkudu da Kiyawa da su gudanar da taron masu ruwa da tsaki da nufin kawar da tashin hankali da kuma dakile duk wani rashin zaman lafiya a yankin,” inji shi.

 

Solacebase

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending