News
Hezbollah ta sanar da kai hari ga sojojin Isra’ila
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hezbollah a ranar Litinin ta bayyana cewa ta kai hari kan wani gini da sojojin Isra’ila ke amfani da shi a arewacin Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ta kai hari kan wani gini da sojojin Isra’ila ke amfani da shi a matsugunin Margaliot da “makaman da suka dace,” inda suka ce sun samu “tabbataccen sakamako.”
Mutane 5 sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa – ‘Yan sanda
Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra’ila ta bayar da rahoton faruwar lamarin a safiyar yau litinin, inda ta ce wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Lebanon ya fada wani gini a garin Margaliot.
Advertisements
