News
Gwamnatin Tarayya Ta Kai Karar Gwamnonin Jihohin Kasar 36 Kara Gaban Kotun Koli
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin tarayya ta kai karar gwamnonin jihohin kasar 36 a gaban kotun koli, bisa zargin yin katsalandan a harkokin kananan hukumomi.
Premium Times ta ruwaito cewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, ne ya shigar da karar don neman cikakken ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi, inda ya bayyana su a matsayin mataki na uku a gwamnatin kasar.
A cikin karar mai lamba SC/CV/343/2024, Ya bukaci kotun koli da ta haramtawa gwamnonin jahohi rusa zababbun shugabannnin kananan hukumomi da kuma nada masu kula da sha’anin mulkin kananan hukumomin ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa irin wadannan ayyuka na gurgunta ‘yancin cin gashin kai da gudanar da ayyukan kananan hukumomi, wadanda suke da muhimmanci ga tsarin mulki da ci gaban kasa.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
