Connect with us

News

Kungiyar Hezbollah Ta Kai Harin Jirgin Sama Mara Matuki Kan Sansanin Sojojin Isra’ila

Published

on

5c472d89 4e97 4546 ac92 833882edc2a3.jpg

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kungiyar Hezbollah ta dauki alhakin harin da wani jirgin sama mara matuki da aka kai kan sansanin soji da ke arewacin Isra’ila a a yau lahadi, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane fiye da 60 a yankin.Harin na zuwa a wani lokaci da mayakan Hezbollah ke ci gaba da gwabza fada da dakarun na Isra’ila a wani yanki na kusa da Lebanon.

Advertisement

Ma’aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a yau Lahadi cewa mutane 51 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a yau lahadi, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu a Lebanon zuwa fiye da 1,300 tun bayan da kungiyar Hezbollah da Isra’ila suka shiga yakin bai daya a ranar 23 ga watan Satumba.

Zamu Nemi Hakkinmu A Gaban Kotu Bisa Cin Zarafi Da Hukumar Hisba Tayi Mana —Unique Guest In

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila ta ce sama da mutane 60 ne suka jikkata a yankin da kungiyar Hezbollah ta ce ta kaddamar da wasu jerin hare-hare na bama-bamai a sansanin horar da sojoji a kudancin Haifa, babban birnin arewacin Isra’ila, inda ta sadaukar da wannan harin ga tsohon shugabanta , Hassan Nasrallah, wanda Isra’ila ta kashe a ranar 27 ga watan Satumba a kusa da Beirut. Kungiyar ta Hezbollah ta ce ta gwabza da sojojin Isra’ila da “makamai masu sarrafa kansu” da “roka” a karshen yammacin ranar a akalla kauyuka hudu da ke kan iyaka da Isra’ila, kuma sun yi wa sojojin kwanton bauna da suke kokarin kutsawa cikin kasar.

Advertisement

Ministan tsaron kasar Yoav Gallant ya bayyana a yau lahadi cewa Isra’ila ba za ta bar kungiyar Hezbollah ta koma yankunan kan iyaka ba, ko da bayan janyewar sojojinta.

AFP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending