Connect with us

News

Zamu Nemi Hakkinmu A Gaban Kotu Bisa Cin Zarafi Da Hukumar Hisba Tayi Mana —Unique Guest In

Published

on

IMG 20241013 WA0009

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Mamallaka Wani Ginin Masaukin Mutane Mai Suna ( Unique Guest In ) Dake Unguwar Danbare a Jihar Kano sun bayyana Cewa Zasu Gurfanar da Hukumar Hisba Ta Jihar Kano a Gaban Kotu Sakamakon Cin Zarafi da Kuma Barna da Suka ce Hukumar ta Hisba Tayi Musu

Advertisement

Mamallaka Ginin Sunce Sun Samar da Wannan Gini ne a Kusa da Sabuwar Jami’ar Bayero Kano Domin baiwa Dalibai Masu Karamin Karfi Damar Samun Masauki Dake zuwa daga sassan Kasar nan harma da Yan kasuwa Dake Zuwa Kano Domin Su Ya-da Zango Amma abin Mamaki shine Yadda Jami’an Hukumar ta Hisba Suka afkawa Wannan Gini Tare da Lalata Musu dukiya harma da awon Gaba da Wasu Muhimman Kayyaki

MAULIDI: Nutsuwa Wajibi Ce Ga Duk Musulmi A Yayin Ambaton Manzon Allah  —Malam Ibrahim Khalil

Daya Daga Cikin Masu Kula da Wannan Gini Mai Suna Nafiu Jibrin, ya Shaida mana Cewa Bai Kamata Hukumar Hisba Ta Rika aiki Batare da Ka’ida ba, tunda dai Akwai Doka Kamata Yayi Hukumar ta Rika bin Doka ba wai Barnata Dukiyar Al’umma ba acewar Nafiu Jibrin Daya Daga Cikin Masu Kula da Wannan Gini

Advertisement

 

Yace Ta Yaya Jami’an Hukumar Hisba Zasu Shigo Wannan Gini da abokan Huldarmu Suke Ciki Kuma su Rika fasa Daki Suna kwashe kayayyaki da Suka hada da akwatunan Talbijin da kwamfuta da kudade da Wayoyi Kuma su Tafi dasu ?

Advertisement

 

Hatta Celling din Sama na Dakunan Wannan Gini sai da suka fasa mana Kuma Suka Tafi abinsu Wannan baza mu lamunta acewar mamallaka Ginin Masauki Mai Suna Unique Guest In Dake Unguwar Danbare

Advertisement

 

Sai dai da Muka Tuntubi Hukumar ta Hisba Ta Jihar Kano kan Wannan Koke, Hukumar tace Hakika ta Ziyarci Wannan Gini Amma Babu wata barna da Tayi acewar Hafizu Adakawa Wanda Shine Shugaban Sashin kula da ayyuka Wato Operation na Hukumar Ta Hisba

Advertisement

 

Sai dai Kuma Tuni Mamallaka Wannan Gini Sun bayyana Cewa sun Kammala Dukkan Shirye Shiryen da suka Kamata domin Gurfanar da Hukumar ta Hisba a Gaban Kotu Sakamakon Barna da Suke Zargin Hukumar Tayi Musu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending