News
KANO: Tsohuwa Ta Yi Barazanar Kai Ƙarar Wanda Ya Shirya Gasar Cin Taliya Da Jikanta Ya Lashe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani matashi ɗan kimanin shekaru 18 mai suna Yahaya Adam, a unguwar Ɓulɓullawa da ke yankin Tukuba na Ƙaramar hukumar Kura ta Kano, ya cinye taliya da Manja da Yaji leda guda nan take yayin wata gasa bayan da ya sanya wayarsa ta hannu da darajarta ya kai nair dubu 18.
An sanya gasar ne yayin da matashin ke tare da abokansa suma ‘yan shekaru 18 zuwa ƙasa, bayan muhawara da suka tafka tsakaninsu kan abinci da aka saya wa wani wanda ta kai ga sanya gasar shi kuma ya basu mamaki kan yadda ya cinye taliyar har da tsuɗe kwano.
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata, Bayan Da Tankar Mai Ta Yi Bindiga A Abuja
A cewar matashin Yahaya, wannan ba wani abun mamaki bane saɓanin yadda wasu ke ganin ba zai iya ba inda ya ƙara da cewa lafiyarsa ƙalau yake jin kansa kuma ko ƙaro wata aka yi zai iya cinye wa.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa bayan ya cinye gasar nan take kakar matashin ta nuna ɓacin ranta game da gasar inda ta shaida cewa duk wani abu da ya faru da shi su ne sanadi tare da ɗauko jami’in tsaro amma da zuwansa ya tafi wanda ya ce lamarin gasa ba’a sasanci akai.
Wanda ya sanya gashar tare da sayan taliyar cike da mamaki ya ce bai yi tunanin Yahaya, zai iya cinye taliyar ba kana ya danƙa masa wayarsa a ƙarshen gasar kuma tare da cewa sun hutashar da kakar maganar abinci a ranar.
Wasu mazauna unguwar Muhammad Usman da Zainab sun ce abun ya basu nishadi ganin yadda ya tashi ƙyam baya cinye taliyar da matashin ya yi tare da ci gaba da harkokinsa inda suka ja hankalin sauran matasa masu sha’awar irin gasar idan sun san ba za su iya ba kar su fara.
