News
Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Yin Titin Jirgin Kasa A Filin Jama’a A Kuyan Ta Inna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wata babbar kotun Kano mai lamba 4 karkashin mai shari’a Usman Malam Naabba, ta bayar da umarnin hana gwamnatin tarayya gina titin jirgin kasa a filayen mutane dake layin Kuyan Ta Inna dake Kano.
Mai shari’a Usman Malam Naabba ya bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman kotun, Lauyan wadanda suka shigar da kara, Barista Umar Usman Dan Baito, ya bayyana cewa addu’ar da aka yi wa wadanda ake karan ita ce ta hana wadanda ake kara yin zagon kasa, da kuma kafa titin jirgin kasa kan kadarorin masu bukata har sai an saurari karar.
Barista Dan Baito ya bayyana cewa kotun da ke karkashin mai shari’a Naabba ta bayar da wannan umarni, tare da hana wadanda ake kara shiga ko kuma kutsa kai cikin lumana na mallakar kadarori daban-daban na mutune a layin Kuyan Ta Inna a Kano. Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 18 ga Nuwamba, 2024.
Wadanda ake tuhumar sun hada da ma’aikatar sufuri ta tarayya, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya, babban hafsan soji, sufeto janar na ‘yan sanda, daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Jami’an Tsaro na Civil Defence na Najeriya, da wani dan kasuwa da ke aiki da sunan kasuwanci.
