News
A hannun talakawa ake karbar mafi yawan harajin Najeriya
Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Tsare-Tsare da Garambawul ga Harkokin Haraji a Najeriya ya bayyana cewa mafi yawan harajin da ake karɓa a Najeriya ana karɓa ne daga hannun talakawan ƙasar.
Shugaban ya ƙara da cewa, ƙasar nan na fama da matsalar zurarewar kuɗin shiga wanda a halin yanzu gwamnati ke ƙoƙarin nemo dabarun da za ta hana zurarewar kuɗin kamar yadda Jaridar Daily Post ta rawaito.
Taron wanda ya kasance na daukacin jihohin tarayya da babban birnin tarayya, hukumar kula da harkokin kudi ta Najeriya, NFIU ta shirya.
Da yake amsa tambayar ‘yan jarida, shugaban kwamitin gyaran haraji ya ce “Ba zan ce Najeriya ta lalace ba, zan ce muna da matsalar kudaden shiga”, ya kara da cewa wannan kalubale da sauran su na daga cikin dalilan taron.
Ya ce domin shawo kan wannan kalubale, dole ne gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su hada kai musamman a fannin bayanai da iya aiki.
Ya kuma jaddada bukatar samar da ingantaccen tattara bayanai masu inganci don baiwa dukkan bangarorin gwamnati damar bunkasa kudaden shiga cikin gaggawa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
