Sports
WANE DAN WASA NE ZAI IYA LASHE KYAUTAR BALLON D’OR TA SHEKARAR 2024?

DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Za a yi bikin gwarazan ‘yan kwallon ƙafa na duniya a Paris ranar Litinin 28 ga Oktoba wannan Shekarar ta 2024.
Wannan ne karo na 68 da za a yi bikin, wanda mujallar France Football ta Faransa ke bayarwa ko wacce shekara tun 1956.
Kyautar Ballon d’Or ita ce wadda ake yi wa kallon mafi daraja da ‘yan wasa ke ci a matsayin ɗaiɗaiku daga ɓangaren maza da mata.
Duk da cewa akwai wasu sauran kyautuka da ake bayarwa yayin bikin daban-daban, duka idanu za su koma kan wanda zai gaji Lionel Messi wanda ya lashe ta 2023 a ɓangaren maza, a ɓangaren mata kuma muga ko Aitana Bonmati za ta sake lashe wannan kyauta
Akwai sunayen mutum 30 cikin jadawalin daga ɓangaren maza da mata:
A ɓangaren maza akwai Ingilawa shida – kyaftin ɗinsu Harry Kane da Jude Bellingham da Phil Foden da Declan Rice da Bukayo Saka da kuma Cole Palmer.
Sai ‘yan wasan da ke taka leda a Ingila da suka haɗa da: Ruben Dias da miliano Martinez da Martin Odegaard da William Saliba.
Wannan ne karon farko tun 2003 da ba a ga sunan Messi ba da ya lashe kyutar sau takwas da kuma Cristiano Ronaldo da ya lashe sau biyar a tarihi ba
A ɓangaren Mata kuwa akwai ‘yan ƙasar Ingila uku Lauren James da Lucy Bronze da kuma Lauren Hemp.
Akwai mata shida daga cikin matan da ke buga Women Super League na Ingila da suka haɗa da ‘yan wasan Chelsea biyu Sjoeke Nusken da Mayra Ramirez, sai ‘yan wasan Manchester City Yui Hasegawa da Khadija Shaw akwai ‘yar wasan Arsenal Mariona Caldentey
Ana bayar da kyautar ne ta hanyar zaɓen da ‘yan jarida ke yi daga kowacce ƙasa cikin ƙasashe 100 na jadawalin Fifa ɓangaren maza.
Ɗan wasan REal Madrid na gaba Vinicius shi ne ke kan gaba da zai iya lashe wannan kyauta a karon farko.
Vinicius mai shekara 24 ya zura kwallo 24 ya bayar da 11 an ci a duka gasanni a bara, yayin da Madrid ta lashe La Liga ta kuma kofin zakarun nahiyar turai karo na 15 a tarihi.
Dan wasan Brazil ɗin ya ci wa Madrid kwallo a wasan ƙarshe na Champions Lig da suka buga da Borussia Dortmund a filin wasa na Wembley a watan Yuni.
Abu guda da zai iya mayar da shi baya shi ne ƙoƙarinsa a BRazil. Ya ci kwallo biyu ne kawai a wasa tara da ya buga a wannan shekarar, kuma ya gaza kai ta mataki na gaba wasa kusa da na ƙarshe a Copa America.
Dan wasan Manchester City Rodri shi ne ke kusa da Vinicius. Mai shekara 28 ya tamaka wa City ta lashe Premier a bara – na huɗu a jere – kuma shi ne ɗan wasan da ya fi kowa ƙoƙari a gasar Euro 2024 da Spain ta cin ye Ingla a wasan ƙarshe a watan Yuni.
Jude Bellingham shi ma na cikin ‘yan takarar biyo bayan ƙoƙarin da ya yi a kakar farko da ya je Real Madrid inda ya ci kwallo 23 a wasa 42 da ya buga.