News
Majalisar Najeriya Ta Tabbatar Da Nadin Sababbin Ministoci Bakwai Akan Mukamansu

DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Majalisar dattatwan Najeriya ta tabbatar da nadin dukkanin ministoci bakwai da shugaba Bola Tinubu ya mika sunayensu ga majalisar a makon da ya gabata domin tantancesu.
Jaridar Punch ta rawaito cewar An tantance sunayen Sababbin ministocin Shugaban Tinubu ne a zauren majalisar dattatwan a ranar Talata.
Wadanda majalisssar ta rantsar dai sun hadar da Nentawe Yilwatda, wanda aka nada domin maye gurbin Betta Edu a matsayin ministar harkokin jin kai da rage talauci ta ƙasa.
Sai Kuma ragowar ministocin Shida Wadanda majalisssar ta da suka hadar da Bianca Odumegu-Ojukwu da aka naɗa a matsayin karamin ministan harkokin waje, Maigari Dingyadi wanda aka naɗa a matsayin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, sai Kuma Jumoke Oduwole a matsayin ministar masana’antu.
Ragowar ministocin sune Idi Maiha a matsayin minista a sabuwar ma’aikatar raya dabbobi, Yusuf Ata a matsayin karamin minista, gidaje da raya birane, sai Suwaiba Ahmad a matsayin ministar ilimi.
Majalisssar dai tayiwa Sababbin ministocin tambayoyi gabanin nadasu akan mukamansu akan irin yaddda zasu tafiyar da ayyukansu sannan sanatoci suka tabbatar dasu akan kujeransu.
Idan ba’amantaba a ranar Larabar da ta gabata ne dai shugaba Bola Tinubu ya kori ministocisa biyar, ya kuma sake nada ministoci 10 a matsayin ministoci, sannan ya tura sunayen ministoci bakwai domin majalisssar dattatwan ta tantancesu.