Connect with us

News

In Ban Da Rashin Sani, Dokar Harajin Shugaba Tinubu Ribar Ƙafa Ce Ga Ƴan Arewa – Jibrin Kofa

Published

on

Yan Arewa Basa Kalubalantar Dokar Ƙarin Haraji Da Shugaba Tinubu Zai YiAbdulmumin Kofa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A yayin da ake cigaba da dambarwa kan batun sake fasalin haraji a Najeriya da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta gabatar wa da majalisun ƙasar domin neman sahalewarsu.

Advertisement

Ana cigaba da samun ra’ayoyi mabambanta da ke nuna goyon baya ko sukar waɗannan ƙudurori.

Ƴan Majalisun Arewa Da Suka Amince Da Dokar Haraji Basa Kishin Arewa – Human Right

Abdulmumini Jibrin Kofa, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Kano ya ce ko kaɗan babu wani abin cutarwa tattare da ƙudurorin dokar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da musu da shi a majalisa.

Advertisement

Kofa ya ce, “na shafe shekaru huɗu a matsayin shugaban kwamitin kuɗi, don haka ba abu ne nake yi da ka ba. In ga kaso kusan 90 da suke cikin wannan sabuwar dokar, abubuwa ne da muka daɗe tun ina ciyaman na kwamitin kuɗi, muke ta ƙoƙarin gwamnatin tarayya ta yi. A canza dokar harajin Najeriya a sanya waɗannan abubuwa kuma waɗannan abubuwa da ake magana, wallahi tallahi ba abubuwa ne da za su cutar da talaka ba.” in ji Kofa.

Haka kuma ya ƙaryata batun da ake na an ƙara wa talaka haraji a wannan doka, inda ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne.

Advertisement

Kofa ya ce, “sake fasalin haraji abu ne da zai shafi dukkan jihohin Najeriya ba wai iya Arewa ba.”

Sannan ya ce akwai alfanu mai yawa da talaka zai samu idan aka tabbatar da wannan ƙuduri. Ya buga misali da cewa, “A tarihin Najeriya wannan ne karon farko da za a cire wa talaka harajin VAT daga kan kayan abinci.”

Advertisement

 

Ya ce hatta harkar ilimi da lafiya duk an cire musu harajin VAT.

Advertisement

 

Har’ila yau ya ce, talaka zai samu tagomashi ta fuskar mafi ƙarancin albashi da aka yi a kwanakin baya, domin duk wanda albashinsa mafi ƙarancin ne, to ba zai biya harajin VAT wanda a yanzu kowa sai ya biya wa kuɗin da yake samu a wata haraji.

Advertisement

 

Kofa ya ce hatta ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa an cire musu harajin VAT gabaɗaya. Hakan na nufin da yawan ‘yan kasuwa ba za su riƙa biya wa kayansu wani haraji ba.

Advertisement

 

MATSAYIN HARAJI GA JIHOHI:

Advertisement

 

Kofa ya bayyana tsarin rabon Harajin da ƙudurin ya ƙunsa a matsayin tsari, “wanda ba cuta ba cutarwa”.

Advertisement

 

Ya ce babban abin damuwa shi ne yadda ake biyan harajin kayayyaki da aka samar a shalkwatar inda kamfanonin suke a jihohin wanda ya ce dokar da aka yi yanzu ta canza wannan.

Advertisement

 

Ya ce daga yanzu duk a inda mutum ya sai kaya, ya yi cinikayya, a wannan jiha zai biya harajin VAT.

Advertisement

 

Ya ce akwai jihohin da za su samu ƙarancin kuɗin shiga na harajin VAT saboda wasu dalilai kuma jihohin nan akwai su a Kudu da Arewa. Don haka, “ban so ace an mai da abin kamar Kudu da Arewa ne ba,” saboda abu ne da ya shafi dukkan jihohin Najeriya.

Advertisement

 

Ɗan majalisar ya buga misali da jihohin Zamfara da Katsina da Yobe da Sakkwato a matsayin wasu daga cikin jihohin da za su iya gamuwa da ƙalubale, inda kuma a Kudu ya ba da misalin jihohi kamar Ekiti da Bayelsa da Osun da Kuros Ribas da Imo.

Advertisement

 

Ya ce kamata ya yi a duba jihohin da ka iya shiga matsala domin ganin yadda za a tallafa musu domin jihohin kudu biyu, Kuros Ribas da Imo sun ne mafi fuskantar wannan barazana.

Advertisement

 

Haka zalika ya ce a wannan dalili ya sa ƙudurin ya zo da wata mafita ga irin waɗannan jihohi inda aka ware kaso 5% na ɗaukacin kuɗin da aka tara daga dukkan jihohin Najeriya wanda kuɗin zai kama kusan biliyan 500 da za a yi amfani da shi wajen tallafa wa jihohi da ake fargabar ba za su iya kai batensu ba.

Advertisement

 

A ce a yanzu ba yadda za a yi amfani da sukari ko siminti ko wani kaya da ke samarwa a wata jiha sannan a ce za saka kuɗin harajin waɗannan kaya a wata jiha daban da sunan a can kamfanonin suke. Sabuwar dokar haraji ta soke wannan, inda ya ce dokar ta tanadi cewa a duk inda ka sai buhun siminti a nan za biya harajin VAT kuma na wannan jiha ne.

Advertisement

 

Ya ce jihohi za su mori kaso 60% ɗari na abin da suka samu a iya jiharsu, inda za a saka kaso 40 a asusun da kuma za dawo daga baya a raba wa kowa.

Advertisement

 

Ya ce dambarwar a kan kaso 60% ne da jihohi za su riƙe inda ake kallon jihohi kamar Oyo Ogun Legas da makamantansu da ake ganin za su samu kaso sittin mai gwaɓi.

Advertisement

 

Kofa ya ce akwai jahilci game da rashin karanta dokar kanta da da ke damun wasu ‘yan majalisa, inda ya ba da misali da wani ɗan majalisa mai hawa biyar wanda ya buga misali ba daidai ba a ƙoƙarinsa na sukar ƙudurin haraji.

Advertisement

 

“Don haka, ko da a jihohin Arewa, akwai waɗanda za su samu fiye da abin da suke samu yanzu kamar jihar Kano da Kaduna, sannan kamar jihohin Kudu, akwai jihohin da ba za su samu abin da suke samu a yanzu ba, amma shi ma ba tabbas. Za su iya samu, za kuma su iya gaza kai wa,” in ji Kofa.

Advertisement

 

Sai dai a yayin da Kofa ke waɗannan kalamai, tuni ƙungiyar gwamnonin Arewa haɗi da sarakuna da majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa da malaman addini daga Arewa sun soki waɗannan ƙudurori tare da nuna cewa sun ci karo da muradansu.

Advertisement

 

Game da ƙudurorin Harajin:

Advertisement

 

Ƙudurori guda huɗun da ake dambarwa a kansu su ne:

Advertisement

 

Game da ƙudurorin sake fasalin Haraji:

Advertisement

Ƙudurorin da ake dambarwa a kan su su ne:

Ƙudurin Dokar Haraji Ta Najeriya 2024

Advertisement

Ƙudurin Dokar Kula da Haraji ta Ƙasa

Ƙudurin Dokar Samar da Hukumar Haraji

Advertisement

Ƙudurin Dokar Samar da Hukumar Haraji ta Haɗin Guiwa

 

Advertisement

Waɗannan ƙudurori ne da shugaban masu rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar a yayin da zama da majalisar dattawa ta yi a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.

 

Advertisement

Wasu na ganin da yawa daga cikin waɗanda suke sukar ƙudurin ba su kai ga karanta cikakken daftarorin dokokin ba.

Sai dai duk da haka, ƙudurorin sun samu tsallake karatu na biyu wanda ka miƙa wa kwamitin kuɗi ƙarƙashin Sani Musa (APC na jihar Neja) domin ɗaukar matakin da ya kamata.

Advertisement

 

Wannan mataki na zuwa ne bayan bayyanar shugaban kwamitin kuɗi da sake fasalin haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele wanda ya bayyana a gaban majalisar dattawa tare da yi wa ‘yan majalisar ƙarin haske kan ƙudurorin.

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending