Connect with us

News

Tsangayar Nazari A Fannin Tsaro Ta Akarrama Amb. Ibrahim Waiya Da Lambar Yabo 

Published

on

IMG 20241201 WA0010

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Tsangayar nazari a fannin tsaro wato The Institute of Security and Strategic Studies ta karrama Amb. Ibrahim Waiya da lambar yabo ta Fellow a taron girmamawa na Kasa akan Kyakkyawan Ayyuka a Fannin Tsaro.

Advertisement

Taron, wanda ya samu halartar manyan baki daga sassan kasar nan, wanda ya gudana a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja, a ranar 30 ga Nuwamba, 2024.

In Ban Da Rashin Sani, Dokar Harajin Shugaba Tinubu Ribar Ƙafa Ce Ga Ƴan Arewa – Jibrin Kofa

Amb. Ibrahim Waiya, wanda shi ne Darakta Janar na Citizens for Development and Education (CDE) kuma Shugaban Sakatariyar Kwamitin Zaman Lafiya Na Jihar Kano wato Kano Peace Committee (KPC), da Nigeria for Peace Project (N4P), da kuma Babban jami’ín gudanar da shirin Gwamna Engineer Abba Kabiru yusuf, a kan inganta rayuwar tubabbu a kan harkar bangar siyasa da daba a jihar kano an karrama shi da wannan gagarumin lambar yabo na Tsangayar tare da wasu mutane ‘yan Najeriya.

Advertisement

 

Wadanda aka karrama su sun hada da:

Advertisement

 

Janar Christopher Musa OFR, Babban Hafsan Tsaron Najeriya,

Advertisement

Hon. Mai Shari’a Edward Amoako Asante, tsohon Shugaban Kotun ECOWAS,

Manjo Janar Johnson A.O. Ochoga Rtd,

Advertisement

H.E. Sanata Injiniya Dave Umahi,

Farfesa Chiedozie Benjamin Okoro,

Advertisement

Dr. Kabiru Adamu, Shugaban Beacon Security and Intelligence LTD, da wasu da dama.

 

Advertisement

Girmamawar da aka yi wa Amb. Ibrahim Waiya na shiga cikin jerin fitattun mutane, ta biyo bayan gamsuwar da tsangayar tayi wajan gudunmawarsa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Tare da gudunmawarsa wajen bunkasa zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano da kuma kasa baki daya, ya bambanta shi a matsayin mutum mai kishin tsaro, zaman lafiya da hadin kan Najeriya, tare da burin ganin Najeriya ta kasance cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Advertisement

Abokan arziki da masoya sun kuma gode wa Tsangayar nazari a fannin tsaro wato The Institute of Security and Strategic Studies bisa girmama wannan gwarzo a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending