Connect with us

News

Ina Fadawa Ya’Yana Mata Duk Lokacin Da Za Suyi Aure Idan Mazajensu Sun Maresu Su Rama –Sarki Sunusi  

Published

on

1733762210406

DAGA KABIR BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya ce a kullum yana gaya wa ’ya’yansa mata cewa idan mazajensu suka mare su suma su rama marin.

 

Advertisement

Sarki Sunusi ya bayyana haka ne a wajen wani taron tattaunawa na kasa kan yaki da cin zarafin mata a mahangar addinin Musulunci mai taken Koyarwar addinin Musulunci kamar Yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.

 

Advertisement

Anayin wannan taro ne lokaci bayan lokaci dan  hadin kan al’umma don kawo karshen cin zarafi tsakanin Mata  wanda cibiyar wayewar Musulunci da tattaunawa tsakanin addinai (CICID) ta shirya. , Jami’ar Bayero Kano (BUK)  dake Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Bincike da Ayyuka (dRPC) tare da tallafi daga gidauniyar Ford.

 

Advertisement

Sarki Sunusi ya ce a rahotannin da suke samu a kotuna kaso 45 cikin 100 ana samun sune sakamakon cin zarafin ya’ya Mata wanda Mazajensu suke musu.

 

Advertisement

Sarkin ya ce babu wata  hujja ko Aya da tazo a cikin alqur’ani wacce tace idan Mata tayiwa Mijinta Laifi ya saka hannu ya mareta.

Idan har muddin Miji yaki cika alkawarin daya daukarwa Yarinya da Iyayenta da Kuma wasu dokoki da yaki cikawa tom ba haramun bane idan Mace ta mari Mijinta.

Advertisement

 

Sarki Sunusi ya ce  ya yi karatun digirin digirgir ne a kan shari’ar iyali, kuma yana  bincike a kan kotuna tara, kotunan Shari’a musulunci  na  Kano. Kashi 41 na shari’o’in a cikin shekaru biyar sun shafi kiyayewa. Kashi 26 cikin 100 na da nasaba da cutarwa. Kuma a cikin wadannan, kashi 45 cikin 100 sun kasance na dukan matan aure, da tashin hankali a cikin gida ne Wanda a ciki dukkansu Mazajensu ne sukai musu dokan kawo wuka.

Advertisement

 

 

Advertisement

“Muna da mata da sassan jikinsu ya karye sannan Muna da mata da hakoransu suka fitce Muna da matan da aka saka  sanduna aka dakesu Muna da mata wadan da sauran matansa suka yi wa daya daga cikin matan duka.

 

Advertisement

Sarkin ya  kara da cewa .dukan matarka ko duka ‘yarka ko dukan mace haramun ne Laifi ne Kada ma mu yi magana game da kyalle ko sandar tauna Haramun ne kawai An haramta. Allah ya ce, dole ne a kawar da dukkan cutarwa Kuma duka, cin zarafin jinsi yana da illa.

 

Advertisement

Nasha fada a baya wanda nasha suka Kuma haryanzu saina cigaba da fada cewa Idan ’ya’yana mata za su yi aure, sai na ce musu, idan mijinki ya mare ki, kada  ki zo gida ki ce min mijinki  ya mare ki  baki rama ba  domin ban aurar da ‘yata ba  wani ya mare ta’ba Idan baka  sonta ka kawai ka dawomin da ita gida a cewarsa.

Shima a nasa jawabin, Daraktan hadin gwiwa da sadarwa Dr Hassan Karofi ya bayyana shekaru 22 na DRPC na tallafawa shugabannin musulmi sama da 200 don tallafamusu  wanda akafarayi  Kasar  Masar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending