Connect with us

News

Kwacen Waya Da Fadan Daba Sun Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano.

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A yayin da aka samu raguwar ayyukan fadan Daba da kuma kwacen Wayoyin mutane a fadin jihar Kano sakamakon sabbin dabarun da Jami’an Tsaro suka bullo da shi .

Sai dai kuma yanzu lamarin fadan Daba yazama wata babbar barazana ga Unguwanne Zango, Kofar Mata, Yakasai da Rimi dake Jihar Kano.

Ina Fadawa Ya’Yana Mata Duk Lokacin Da Za Suyi Aure Idan Mazajensu Sun Maresu Su Rama –Sarki Sunusi  

SolaceBase ta ruwaito cewa Fiye da bata-gari 100 ake zargin sun kutsa kai cikin shaguna fiye da biyar a unguwannin Zango, Kofar Mata, Yakasai, da Rimi, inda suka lalata motoci kuma suka sace dukiyar mazauna yankin yayin rikici.

A cewar mazauna yankin, rikicin ya fara ne da yammacin Lahadi bayan wasan kwallon kafa tsakanin Kano Pillars da Katsina United a filin wasa na Sani Abacha.

Rahotanni na nuni da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu yayin wannan rikici.

Advertisement

Halifah Auwal, wani mai kasuwancin CAJIN WAYA a yankin Zango, ya ce bata-garin sun kutsa cikin shagan sa sun sace fiye da wayoyi 40 da kwastomomi suka kawo cajin waya.

“Da safiyar yau, yayin da nake ci gaba da kasuwanci a shagona, wasu bata-gari sun kai mani hari.

Na tsallake da kyar. Wadannan miyagun sun sace wayoyi sama da 40, kwamfuta guda daya, ,” inji Auwal.

“Yanzu haka, mutane da ba su san abin da ya faru ba suna zargina da sakaci kan wayoyinsu.

Haka zalika Bata-garin sun kuma kai hari kan wani masallaci, inda suka hana jama’a yin sallah tare da lalata tankunan ruwa guda uku da ake amfani da su wajen alwala.

Wani mutum da abin ya shafa, Musa Muhammad, mai sayar da kayan marmari, ya ce bata-garin sun sace babur dinsa wanda yake dogaro da shi wajen zirga-zirga.

Advertisement

“Yayin da nake cikin kasuwanci, wadannan bata-gari sun kai mini hari suka kwace babur dina. Wannan babur din shine hanyar zirga-zirgata tsakanin gida da kasuwa,” inji Muhammad.

Shugaban Zango a karamar hukumar birni ta Kano, Muhammad Rabi’u, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rikicin ya samo asali ne bayan wasan kwallon kafa, yana mai zargin bata-garin da ba ‘yan yankin ba ne.

A matsayina na shugaba, koyaushe muna jan hankalin matasanmu da su nisanci irin wadannan mutane don kaucewa zubar da jini,” inji Rabi’u.

Ya soki gwamnati saboda gazawa wajen magance rikice-rikicen da ke faruwa yayin wasannin kwallon kafa a wannan yanki.

“Ya zama ruwan dare ga bata-gari su taru su kai hari kan jama’a duk lokacin da aka yi wasan kwallon kafa a filin wasa na Sani Abacha. Gwamnati dole ta tashi tsaye ta magance wannan matsala,”

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Salman Dogo Garba, ya ziyarci wurin da abin ya faru a ranar Litinin inda ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu a harin.

Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Kofar Mata a yammacin Litinin domin hana faruwar irin wannan a nan gaba.

Ya kara da cewa kwamishinan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending