Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Daya Wajen Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje Cikin Watanni 9

Published

on

Gwamnan Kano Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Daya Wajen Tafiye tafiye Zuwa Kasashen Waje Cikin Watanni 9.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kashe Naira 1,064,570,891.79 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje cikin watanni 9.

A cewar SAHARA REPORERS duk da wannan makudan kuɗaɗe da gwamnan na Kano ya kashe wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, amma bai janyo ko da mutum daya da ya zo Kano ya zuba hannun jari a jihar ba.

Kwacen Waya Da Fadan Daba Sun Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano.

Jaridar ta ruwaito cewa gwamnonin jihohin Kwara, da Borno sun kashe jimillar N3,880,451,077.65 kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da harkokin sufuri cikin watanni tara, amma su janyo ko da mutum daya da ya zo Jihohin ya zuba hannun jari a jihar ba.

Haka zalika, duk da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihohin arewacin Najeriya.

Rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar na uku na 2024 ya kuma bayyana cewa jihohi 32 daga cikin 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) ba su janyo wani jarin kasashen waje ba cikin watanni tara na farko na 2024, wanda ya karu daga jihohi 27 a shekarar 2023 gaba ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending