Connect with us

News

Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Ma’aikatan Haraji 5 Bisa Zargin Wawure Naira Biliyan 1.2 A Katsina 

Published

on

Hukumar EFCC Ta Kori Jami’anta 27 Bisa Laifin Zamba Da Rashin Da

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta  EFCC ta  kama ma’aikatan haraji a jihar Katsina bisa zargin zambar kudi  naira biliyan N1,294,337,676.53 da suka shigo wa jihar daga hukumar lafiya ta duniya da sauran wasu hukumomin daga  ketare.

Advertisement

Wadanda ake zargin sun hada da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da Nura Lawal Kofar Sauri.

Al,umma Na Takaicin Yadda Masu Gidajen Burodi Suka Ki Saukar Da Farashi Kayansu Duk Da Fulawar Ta Sauka

An kama su ne biyo bayan wani koke da gwamnatin jihar Katsina ta shigar na cewa wadanda ake zargin sun hada baki tare da karkatar da kudaden da suka kai N1,294,337,676.53 daga hannun hukumar lafiya ta duniya.

Advertisement

Binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa Nura Lawal da kamfanin sa na ”NADIKKO” da su ake amfani wajen karkatar da kudaden da aka wawure,wadannan kudade da aka wawure an gano su ne a asusun bankuna daban daban na wadanda ake zargin.

Yanzu haka dai wadanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar EFCC shiyyar Kano kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending