News
Mahalarta Ɗaurin Aure 19 Daga Kano Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Filato
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mahalarta ɗaurin aure mutum 19 daga Jihar Kano sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota a yankin Kwanar Maciji da ke Ƙaramar Hukumar Pankshin a Jihar Filato.
Mutum 11 daga cikinsu sun tsallaka rijiya da baya da raunuka a haɗarin da ya ritsa da su a yayin da suke hanyar komawa gida bayan ɗaurin auren da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a ranar Asabar kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Ma’aikatan Haraji 5 Bisa Zargin Wawure Naira Biliyan 1.2 A Katsina
Shugaban Ƙaramar Hukumar Pankshin, John Dasar, ya bayyana cewa motar matafiyan ta kama da wuta ne, amma an yi nasarar ceto direban da wasu fasinjoji.
Ya ce, “an ceto mutane 11 amma mutane 19 sun kone ƙurmus ba za a iya gane su ba, saboda bayan mutane sun zo ana ƙoƙarin ceto fasinjojin ne motar ta kama da wuta, ta cinye ragowar.”
Ya ce an kai waɗanda suka tsira Babban Asibitin Pankshin inda ake duba lafiyarsu.
