News
Ɗaliban Sakandare A Ƙasar Saudiyya Za Su Koma Amfani Da Jallabiyya A Matsayin Kayan Makaranta
DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN
Ma’aikatar Ilimi a ƙasar Saudiyya ta tilasta wa ɗaliban makarantun sakandaren gwamnati da masu zaman kansu saka kayan garganiya a matsayain kayan makaranta.
Hakan ya biyo bayan umarnin Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman na sauya kayan makarantar zuwa jallabiyya da sauran tufafin Larabawa don ƙarfafa al’ada da kuma kishin ƙasar.
Advertisements
