Connect with us

News

Wani Magidanci Ya Guntule Wa Matarsa Hannu Da Adda Bisa Zarginta Da Aikata Zina 

Published

on

DAGA KABIR BASIRU FULATAN

 

Rundunar Ƴan sandan jihar Enugu ta tabbatar da kama wani magidanci mai suna Sunday Echege da laifin guntile hannun matarsa

 

Magidancin mai kimanin shekaru 33 ya yanke hannun hagun matar tasa mai suna Chinonso Echege da adda bisa zarginta da ya’yi da aikata zina.

 

Advertisement

Kakakin rundunar Yan Sanda Jihar Enugu Daniel Ndukwe shine ya sanar da haka a wata takarda daya fitar ga manema labarai a makon Jiya.

 

ya ce Echege ya aikata hakan a cikin gidansa dake kauyen Ibagwa-Agu a karamar hukumar Nsukka.

 

Sai dai kakakin rundunar Yan sandan Ndukwe bai fadi Ranar da abin ya faru amma Ya ce Jamia’ansu dake karkashin rundunar Okpuje ne suka kama magidancin ranar Lahadin makon jiya.

 

Advertisement

Kakakin ya ce jami’an tsaron sun kama Echege ɗauke da addan da ya guntile hannun matarsa da shi.

 

Ya ce Echege na tsare a ofishinsu kuma idan sun kammala bincike za su kai magidancin kotu domin yanke masa hukunci.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending